Gwamnan Gombe ya bada umarnin rufe dukkan gidajen gala a jihar.

Gwamnan Gombe Inuwa Yahaya ya bada umarnin rufe dukkan gidajen gala a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi, shi ne ya sanar da hakan yana mai cewa an ɗauki matakin ne bayan ƙorafe-ƙorafe daga jama’a kan “ƙaruwar ayyukan rashin tarbiyya da aikata laifuka da kuma taɓarɓarewar tsaro” a irin waɗannan kulob-kulob na dare.

Wata sanarwa da mai magana da gwamnan jihar ya fitar ta ce an umarci ‘yan sanda da rundunar tsaron farar hula da jami’an tsaro na Operation Hattara su tura mutanensu don cika umarni da tabbatar da aiki da umarnin.

Haka nan, akwai Gidajen Gala na garin Kuri, da ƙauyen Lubo da Kurba a Yamaltu Deba, da Tauraren Wash a kan titin zuwa Bauchi, da Gidan Gombe, da Gala a garin Bajoga.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *