“An shirya kammala aikin titin Legas zuwa Ibadan nan da tsakiyar watan Satumba” – FG

Ministan ayyuka, Dave Umahi, yace an shirya kammala aikin titin Legas zuwa Ibadan nan da tsakiyar watan Satumba,  bayan da aka fara aikin sake gina hanyar data kasance ta yau da kullum.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara daya kai wuraren da aka kammala ayyukan gwamnatin tarayya a jihar Legas.

Ya fara rangadin ne a wajen titin Marina, a tsibirin Victoria Island, wanda aiki ne da gwamnatin tarayya ta gina a karkashin shirin SUKUK na tallafin kudi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *