Hukumar hana fasa kwauri ta kasa custombirnin  reshen Fatakwal a jihar Ribas ta sanar da samar da kudaden shiga na Naira biliyan 57.4 tsakanin watan Janairu zuwa Yuli na wannan shekara.

Kwanturolan yanki na daya, Chedi Wada, ne ya sanar da hakan yayin wani taron manema labarai a Fatakwal a karshen mako.

Ya bayyana cewa adadin ya haura kaso 10 cikin  100 idan aka kwatanta da kudaden shigar da hukumar ta samu adaidai lokacin na shekarar data gabata.

Kwanturolan yace hukumar ta gudanar da bincike mai zurfi ta gano tare da tsare kwantenonin da aka bayyana.

Ya kuma gargadi masu fasa kwauri dasu gujewa hukumar yanki ta Fatakwal, yana mai cewa dole ne a kama irin wadannan kwantonin, sannan a kama masu laifin tare da gurfanar dasu a gaban kuliya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *