Kwastam sun cafke wiwi da ya kai kimanin naira miliyan 170 a Kebbi

Hukumar Hana Fasa Kwauri ta ƙasa Kwastam a Jihar Kebbi ta ce ta yi nasara cafke haramtattun kayayyaki da kudinsu ga kai kimanin Naira Miliyan 170 a Jihar.

Kwanturolan Hukumar Ben Oramalugo ne ya sanar da haka ga manema labarai a ranar Asabar a Birnin Kebbi fadar gwamnatin Jihar Kebbi.

Ya ce hukumar ta yi nasarar cika hannunta da ƙullin wiwi kima 400 da kuma pakitin ƙwayar magani na Diazepam 98.

Wannan kame da kwastam din ta yi cikin kwanaki goma, sun haɗa da katan goma na garin angur, sa fatar jaki kimanin 1000 da gwanjo da kuma litar mai 300 da kuma mota ƙirar Toyota da ake safarar kayayyakin.

Da yake damƙa muggan ƙwayoyin ga hukumar hana sha da fataucjn muggan ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA, Kwanturolan Kwastam din sun yi wa kayayyakin kuɗi da ya kai kimanin naira miliyan 170.

“Idan ba ku manta ba, kwanaki gima da suka gabata wato ranar 14 ga Agusta yayin da muka gana da manema labarai mun fada muku cewa ba za mu duk wani mai sumogilin din haramtattun kayayyaki ya sha iska ba, musamman masu safarar muggan ƙwayoyi da kuma abubuwa dake da hatsari ga lafiyarmu da kuma tattalin arzikin ƙasa”.

“A saboda haka ne muka baza jami’anmu a lungu da saƙon jiha don yin samame tunda akwai masu fikira cikinsu”.

Daga bisani Ben Oramalugo ya bayyana kaɗuwarsa bisa yadda suka yi asarar jami’ansu biyu yayin samemen, inda ya bayyanasu a matsayin masu ƙwazo da hazaka.

“Abin baƙin alhinin da ya faru da mu a ranar 24 ga watan Agustan 2023 jami’anmu dake aiki a kan hanyar Bunza zuwa Koko zuwa Dakin Gari shn rasa rayukansu – a don haka muku musu fatan Allah Ya jikansu”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *