Kungiyar Kare Hakkokin Tattalin Arziki SERAP ta ba Tinubu sa’o’i 48 da ya janye dakatarwar da ya yiwa wasu kafafen yaɗa labarai

Kungiyar Kare Hakkokin Tattalin Arziki SERAP, ta bayar da wa’adin sa’o’i 48 ga shugaban kasa, Bola Tinubu, kan hana wasu kafafen yada labarai 25 daga shiga Aso Rock.

Kolawole Oluwadare, Mataimakin Daraktan SERAP ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi.

SERAP dai na mayar da martani ne kan janye amincewa ga kafafen yaɗa labarai 25 daga yin aiki a fadar shugaban kasar.

A cewar kungiyar, haramcin ya hada da jaridar Vanguard, da Galaxy TV, Ben TV, MITV, ITV Abuja, PromptNews, ONTV, da Liberty.

SERAP ta bukaci Tinubu da ya fito bainar jama’a ya umurci jami’ai a fadar shugaban kasa da su janye dokar.

Ya bayyana cewa ‘yancin yada labarai shi ne ginshikin dimokuradiyyar Najeriya.

SERAP ta ce tilas ne a dage haramcin da aka sanya wa kafafen yada labarai domin amfanin jama’a da kuma bin diddigi.

“Za mu yi godiya idan an dauki matakan da aka ba da shawarar a cikin sa’o’i 48 da karɓa da/ko buga wannan wasiƙar.

“Idan har ba mu ji ta bakinku ba, SERAP za ta yi la’akari da matakan da suka dace na shari’a don tilasta wa gwamnatin ku biyan bukatarmu don amfanin jama’a,” in ji ta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *