Kungiyar AROGMA, da haɗin gwiwar NNPCL na shirin gayyato kamfanonin kasashen waje don samar da sauyi zuwa amfani da iskar gas

Kungiyar Dillalan Man fetur da Iskar gas ta Arewa, AROGMA, da haɗin gwiwar karamin mai na NNPCL shirin gayyato kamfanonin kasashen waje don samar da sauyi zuwa amfani da iskar gas, musamman a arewacin Nijeriya.

Sabon shugaban AROGMA, Bashir Ahmad Dan-Mallam ne ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai a Abuja

A cewar Dan-Mallam, AROGMA, tare da hadin gwiwar NNPCL na shirin gayyato kamfanoni daga Qatar, Turkiyya, Jamus da Indiya domin samar da iskar gas a Najeriya.

Ya bayyana cewa, AROGMA ta riga ta tuntubi abokan huldar su na kasashen waje kuma tana nazarin shawarwarin su daban-daban.

Shugaban ya yi nuni da cewa, aikin zai zama babbar nasara ga Nijeriya, kuma zai zama wani muhimmin ci gaban kasar nan musamman yankin Arewa.

A cewar Dan-Mallam, aikin zai sauƙaƙa tsadar rayuwa da cire tallafin man fetur ya haifar, musamman a Arewacin Nijeriya.

Ya kuma yabawa hukumomin NNPCL bisa kokarin shiga tsakani don samar da aikin da kuma duk wasu harkokin masu ruwa da tsaki na ɓangaren mai.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *