Najeriya ta zamo kasa ta 11 da akafi kashe kudi a yanar gizo gizo

A daidai lokacin da yan kasar nan ke kukan matsin rayuwa ,Yanzu Najeriya ta zamo Kasa Ta 11 da akafi kashe kudi a yanar gizo gizo ko Internet a turance

Hukumar Kula da Harkokin Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce Najeriya ce kasa ta 11 a yawan masu amfani da intanet a duniya,da kashe kudin Data dan shiga yuanar Gizo Gizo sannan Najeriya ce  ta bakwai a yawan masu amfani da wayar salula.

Shugaban hukumar, Farfesa Umar Garba Dambatta ne ya bayyana hakan a yayin bude wani taro kan fasahohin sadarwa na zamani a yammacin jiya  Alhamis a Abuja.

Dambatta, wanda shugaban kamfanin adana bayanai na Spectrum, Abraham Oshadami, ya ce alkaluman da hukumar NIR ta tattara sun nuna yawan amfani da intanet na taka rawa wajen bunkasa tattalin arzikin duniya.

Ya ce NIR ta duba kasashe 131 a bangarori hudu da suka hada da kayayyakin fasaha da shugabanci da jama’a da kuma tasirinsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *