Gwamnatin Tarayya zata kammala aikin titin Kano-Zaria-Kaduna-Abuja cikin ƙanƙanin lokaci

Ministan ayyuka, David Umahi, a ranar Alhamis, ya ba da tabbacin gwamnatin tarayya na kammala aikin titin Kano-Zaria-Kaduna-Abuja a kan kari.

Ministan ya bayyana hakan ne a lokacin da mataimakiyar gwamnan jihar Kaduna, Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ta tarbe shi a madadin gwamna Uba Sani a ziyarar da ya kai jihar

Umahi ya ce, “Mun zo Kaduna ne bisa umarnin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan wannan muhimmin aiki.

“Shugaban kasa ya umarce ni da kaina in zo in duba wannan hanyar Kaduna zuwa Abuja in kai rahoto gare shi.”

Ministan ya yabawa gwamnatin jihar Kaduna bisa kokarin da take yi wajen inganta harkokin tsaro a jihar.

A nasa jawabin, mataimakiyar gwamnan ta bayyana cewa, samar da ababen more rayuwa na tituna shine mafi muhimmancin kadarorin jama’a da kuma wakili na hadin kan al’umma.

Ta kuma yi kira ga ma’aikatar ayyuka ta tarayya da ta tabbatar da ganin an gaggauta kammala aikin hanyar Abuja zuwa Kaduna zuwa Zariya bisa la’akari da dabarunsa, inda ta ce har yanzu ba a gama kammala aikin titin Eastern bye-pass da aka fara a shekarar 2002 ba.

Ta kara da cewa, idan aka kammala hanyoyin za su inganta harkar tsaro da harkokin tattalin arziki a yankin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *