Tinubu ya sake tura tawagar malaman Musulunci zuwa Nijar domin sake tattaunawa da jagororin juyin mulkin ƙasar.

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya sake tura tawagar malaman addinin Musulunci zuwa jamhuriyar Nijar domin sake tattaunawa da jagororin juyin mulkin ƙasar.

Tinubu ya yanke shawara sake aika tawagar malaman ne a wannan rana bayan ganawa da manyan malaman musuluncin ƙarƙashin jagorancin Sheikh Dahiru Bauchi.

Makonni biyu da suka gabata ne malaman suka ziyarci jamhuriyar Nijar, inda suka gana da shugaban mulkin sojin ƙasar Janar Abdourahamane Tchiani.

Shugaba Tinubu ya yanke shawarar ne a matsayinsa na shugaban ƙungiyar Ecowas.

Ecowas tayi ta ƙaƙabawa Nijar takunkumai tun bayan juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi ranar 26 ga watan Yuli.

A ƙarshen mako ne tawagar Ecowas ƙarƙashin jagorancin tsohon shugaban mulkin sojin Najeriya Janar Abdussalmi Abubakar mai ritaya, ta kai ziyara ƙasar a kokarin shiga tsakanin ƙungiyar da sojojin Nijar, inda ta samu ganawa da hamɓararen shugaban ƙasar Mohamed Bazoum da shugaban mulkin sojin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *