Matawalle ya sha alwashin tabbatar da ya baiwa masu sukar nadinsa a matsayin ministan tsaron Najeriya kunya.

Yan Najeriya da dama, musamman a shafukan sada zumunta na yanar gizo, sun yi ta tafka muhawaraa kan mukamin da aka baiwa Mista Matawalle saboda kasa magance matsalar rashin tsaro a jihar Zamfara.

Sai dai tsohon gwamnan na Zamfara wanda ya yi jawabi a wajen liyafar da aka shirya masa a Abuja, ya bayyana kwarin guiwar magance matsalolin tsaro da kasar nan ke fuskanta.

Mista Matawalle ya ce na dade ina jin wasu suna cewa yayana Badaru [Ministan tsaro] dani kaina bamu da cancantar zama ministocin tsaro,wadannan mutanen ba su ma fahimci mene ne tsaro ba.

Saboda haka, ba a nan ne matsalar take ba, abin da ya fi muhimmanci shi ne jajircewa, jajircewar mutum, da damarsa.

Lokacin da nake gwamnan jihar Zamfara mun dauki dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron jihar.

Akwai lokacin da muka yi kwanaki 100 ba tare da wani kalubalen tsaro ba. Mun kuma shafe watanni 9 ba tare da an cutar da ko mutum daya ba.

Dukkan matakan da na dauka na dakile matsalolin tsaro a jihar Zamfara, dole ne na fara aiwatar da hakan, sannan sauran gwamnonin sun bi sawu.wannan shi ne saboda ina da kyakkyawar fahimta game da al’amuran tsaro.

Ina da albishir ga al’ummar Jihar Zamfara cewa ba zan ba su kunya ba. Na yi imanin cewa da taimakon Allah, za mu iya shawo kan matsalolin tsaro.

Wadanda suka ce ni da Badaru ba za su iya ba, za su ji kunya za su ga cewa Allah ne ke yin aikin ba su ba.

A da, muna neman taimako. Amma yanzu muna da damar taimakawa wasu, Matawalle ya kara da cewa.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya nada tsohon gwamnan Jahar Jigawa Muhammad Badaru a matsayin ministan tsaro yayinda ya nada Bello Muhammad Matawalle a matsayin karamin ministan tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *