“Gwamnatin Tinubu ba ta nufin komai ga ƙasar sai alheri” – Oluremi Tinubu

Oluremi Tinubu ta tabbatar da cewa gwamnatin Tinubu ba ta nufin komai ga ƙasar sai alheri, duk da wahalhalun da ƴan ƙasar ke ciki saboda cire tallafin man fetur.

Remi ta buƙaci ƴan Najeriya su dubi irin nasarori da za a samu nan gaba, ba kawai ga ƙalubalen da ake fama da shi a yanzu ba, inda ta ce akwai nasara mai kyau a gaba.

Ta bayyana ne lokacin da ta karɓi baƙuncin matan hafsoshin tsaron Najeriya da ta babban sufeton ƴan sanda waɗanda matar babban hafsan tsaro Mrs Oghogho Musa ta jagoranta.

Mai ɗakin shugaban Najeriyar ta ce gwamnatin mijinta na yin duk abin da ya kamata don tabbatar da ganin ta rage wa ƴan ƙasar raɗaɗin da suke ciki bayan janye tallafin fetur.

 Ta ƙara da cewa ƴan Najeriya za su fara cin moriyar manufofin gwamnatin matuƙar abubuwa suka fara daidaita.

Ta ce kundin ayyukan gwamnatinsu na Renewed Hope, shi ma yana mara wa gwamnati, don haka ta roƙi goyon baya daga wajen matan hafsoshin tsaron.

Tace zasu tabbatar da ganin tattalin arzikin Najeriya, ya ci gaba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *