Badaru da Matawalle sun fara aiki a hedkwatar ma’aikatar tsaro ta tarayya .

Sabon ministan tsaron Najeriya, Muhammmad Badaru Abubakar da takwaransa, Dakta Bello Matawalle sun fara aiki a hedkwatar ma’aikatar tsaro ta tarayya .

A jawabinsa bayan karɓar ragamar aiki daga Dakta Ibrahim Kana, Babban Sakataren ma’aikatar, Badaru ya ce zai sake duba rahotannin da aka gabatar a baya dangane da halin da tsaro yake ciki a ƙasar nan

Ya ce zai yi haka ne da zimmar ganin an daƙile matsalar rashin tsaro da kawo zaman lafiya a faɗin ƙasar.

Ministan ya ce ba za su ci amanar da Shugaba Bola Tinubu ya damƙa musu ba, don haka ya buƙaci hafsoshin tsaron ƙasar nan dasu  gabayar da bayanin abubuwan da suke buƙata da za su taimaka wajen kawo ƙarshen matsalar tsaro a Najeriya.

Yace a  shirye shugaban ƙasa yake domin basu  dukkan goyon baya a yunƙurinsa na ganin mun samu nasara, saboda mutum ne mai hazaƙa wanda ba ya son a samu gazawa.

Badaru ya tabbatar da cewa jagorancinsu zai kawo gagarumin canji a ɓangaren tsaron Najeriya, inda ya ce ba zai yi wasa da muƙamin nasa ba.

Shi ma a jawabinsa, ƙaramin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ce dakarun Najeriya sun nuna ƙwazo da jajircewa ta musamman a tsawon lokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *