An sake gurfanar da Emefiele  a gaban kotu yau Laraba

An sake gurfanar da  gwamnan Babban Bankin Najeriya da aka dakatar, Godwin Emefiele  a gaban kotu yau Laraba kan tuhumar wasu zarge-zargen da suka shafi almundahar kuɗi da ya kai kusan naira biliyan bakwai.

Gwamnatin Najeriya ta kai ƙarar dakataccen gwamnan Babban Bankin gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja cikin makon da ya gabata domin fuskantar sabbin tuhume-tuhume.

A makon da ya gabata ne ya kamata tsohon gwamnan bankin ya bayyana a gaban kotu, to amma hakan ba ta ba samu ba.

Sakamakon roƙon da lauyan gwamnati Muhammed Abubakar ya yi wa kotun na ɗage zaman saboda ɗaya daga cikin waɗanda ake ƙarar Sa’ adatu Yaro ba ta da lafiya.

Gwamnatin Najeriya dai na zargin Emefiele da laifuka 20 da suka shafi almundahanar kuɗi da haɗin baki da bayar da cin hanci da fifita makusantansa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *