Wike ya sha alwashin kawo karshen kiwo a fili a Abuja

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sabon ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike ya sha alwashin kawo karshen kiwo a fili a cikin Abuja, inda ya ce ba za a iya jurewa irin wannan.

A cikin wani faifan bidiyo da AIT ta wallafa, Wike ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta tuntuɓi makiyaya, yana mai cewa, “Ba za mu bar shanu a cikin Abuja ba”.

Wike, tsohon gwamnan jihar Ribas ne ya bayyana hakan a wata ganawa da manema labarai a Abuja ranar Litinin, jim kaɗan bayan rantsar da shi, kamar yadda gidan talabijin na Channels ta ruwaito.

Sun ƙara da cewa, tsohon gwamnan jihar Ribas ya ce makiyaya za su iya kiwon shanu a wajen birnin amma kuma ba za a bari su ci ciyawar da ake amfani da ita wajen ƙawata birnin ba .

“Za mu tuntuɓi makiyayan domin mu ga yadda za mu daina (kiwo a fili) saboda ba za mu iya barin shanu a cikin gari ba,” in ji shi a wajen taron da aka yi a unguwar Garki da ke Abuja.

Wike ya kara da cewa:

“Suna iya zama a wajen birnin saboda ciyayi suna wajen birnin. An dasa ciyayi a cikin birnin domin ƙawata birnin. Ba wanda za su ci ba ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *