Sabon Ministan FCT yayi barazanar fara rushe gidajen da aka gina ba bisa ka’ida ba a Abuja.

Gwamnatin tarayya tayi barazanar fara rushe gidajen da aka gina ba bisa ka’ida ba a Babban Birnin Tarayyar Abuja.

Ministan Abuja, Nyesom Wike, wanda ya bayyana haka a jawabinsa na farko a ofishin Hukumar bayan shugaba Bola Tinubu ya rantsar da su ya kuma sha alwashin yin watsi da tsarin da ke kawo cikas ga gine-ginen a babban birnin.

Nyesome Wike ya kuma yi alkawarin cewar hukumar babbar birnin za ta duba hanyoyi daban-daban na zubar da shara domin tabbatar da tsaftar birnin tare da yin kira ga  wadanda suka mallaki filaye ba tare da sun gina ba da su gaggauta yin hakan domin hukumar sa ba za tayi kasa a gwiwa ba wajen soke duk wata takardar mallaka fili da aka bayar ba tare da an gina filin ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *