El Rufa’i ya shawarci ECOWAS akan illolin dake tattare da amfani da karfin soji wajen warware takaddamar juyin mulkin da sojojin suka yi a jamhuriyar Nijar.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El Rufa’i, ya shawarci kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin afrika  ta ECOWAS akan illolin dake tattare da amfani da karfin soji wajen warware takaddamar juyin mulkin da sojojin suka yi a jamhuriyar Nijar.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na tuwita, Nasir el-rufai ya bayyana akwai bukatar kungiyar ta Ecowas ta jajirce wajen neman hanyoyin da za tayi amfani da su domin warware lamarin ba tare da an gwabza yaki ba, yana me cewa yakin da kungiyar ta ecowas ke ikirarin gabatarwa tamkar yaki ne tsakanin Najeriya da Nijar, kuma yakin sai yafi shafar kasashen biyu ta kowacce fuska.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *