Tinubu ya rantsar da ministoci 45 a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya rantsar da ministoci 45 a fadar shugaban kasa dake Abuja.

A cikin takaitaccen jawabinsa shugaba Tinubu ya ce an zabo ministocin ne a tsanake saboda kyawawan ayyukansu.

Ya kuma gargade su da cewa kada su dauki kan su a matsayin ministoci na kabilanci ko na addini, sai dai su dauki kansu a matsayin ‘yan majalisar zartarwa ta tarayyar Najeriya.

Bikin wanda ya dauki tsawon sa’o’i biyu da rabi ya gudana ne karkashin kukawar mai baiwa Tinubu shawara kan harkokin yada labarai Aguri Ngelale.

Da farko ya karanta takardar sunayen ministocin, sannan aka rantsar da su, inda suka sanya hannu kan takardar rajista, inda saka yi musabaha tare da daukar hoto da shugaban kasar.

Idan dai za a iya tunawa a ranar 7 ga watan Agusta, majalisar dattawa ta tabbatar da ministoci 45 daga cikin 48 da shugaban kasar ya aika.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *