Rundunar ‘yan sandan Kano ta haramta duk wata zanga-zanga a jihar.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano, ta sanar da haramta duk wata zanga-zanga a jihar, ba tare da bata lokaci ba.

Kwamishinan ƴan sandan jihar  Useni Gumel ne ya bada umarnin da safiyar yau Litinin. Hakan ya biyo bayan bayanan sirri da rundunar ta samu cewa bangarorin biyu na jam’iyyun NNPP da APC, sun tara jama’a domin gudanar da zanga-zanga, ba nisa ka’ida ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *