DSS ta kame Manajan Hukumar Jiragen Kasa ta Abuja-Kaduna dake Kaduna

Hukumar tsaro ta DSS ta kame Manajan Hukumar Jiragen Kasa ta Abuja-Kaduna dake Kaduna, Pascal Nnorli, biyo bayan fallasa sanarwar gargadin yiwuwar kai harin ta’addanci a kan hanyar jirgin Abuja zuwa Kaduna.

Wata majiya mai tushe a Hukumar Jiragen kasa ta Najeriya ta shaida cewa an kama manajan ne tare da Manajan Ayyuka, Victor Adamu da wasu ma’aikatan.

A ranar Larabar da ta gabata ne hukumar tsaro ta farin kaya ta DSS ta fitar da sanarwar tsaro ga hukumar kula da zirga-zirgar jiragen kasa ta Najeriya a kan wani shiri na ‘yan bindiga na kai hari kan hanyar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna a kowane lokaci.

A cikin wata takarda mai dauke da sa hannun Daraktan DSS na rundunarta dake babban birnin tarayya Abuja R.N. Adepemu, rundunar DSS ta gargadi fasinjojin jirgin da su kasance masu kula da tsaro da kuma taka-tsan-tsan.

Wata majiya daga hukumar kula da sufurin jiragen kasar ta yi da’awar cewa takardar, wacce ke da cikakkun bayanai masu mahimmanci game da harin, an aika ta zuwa ga Manajan Darakta na hukumar NRC, yana mai jaddada cewa ta yi gargadin cewa idan har wasikar ta fito, zai iya kaiwa ga kama su.

Lokacin da aka tuntube shi, Manajan Darakta, NRC, Fidet Okhiria, ya ƙi yin tsokaci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *