Ku bayyana kadarorin ku ko ku fuskanci takunkumi — CCB ga ma’aikata

Hukumar Code of Conduct Bureau CCB ta bukaci ma’aikatan hukumar babban birnin tarayya FCTA da su bi ka’idar aikin gwamnati, ko kuma su fuskanci hukunci.

Hukumar tace Musamman ma’aikatan FCTA da su tabbatar da bayyana kadarorin su cikin lokaci domin tabbatar da gaskiya da rikon amana, kamar yadda ofisoshin gwamnati ke rike da amana a madadin ‘yan kasa.

Daraktan hukumar CCB na FCT, Suleiman Usman ne ya bayyana hakan a wani taron wayar da kan jama’a na yini daya da aka gudanar a Abuja.

Usman ya lura cewa har yanzu da yawa daga cikin ma’aikatan gwamnati ba su san wasu bayanai da ayyukan da ake sa ran za su yi ba, wanda hakan ne ya sa ba tare da saninsu ba sai suka koma dai-daita baragurbi a cikin tsarin.

Ya kuma nuna takaicinsa kan yadda ma’aikatan gwamnati ke amfani da lokutan ofis wajen gudanar da sana’o’i masu zaman kansu, inda ya ce yayin da CCB za ta ci gaba da hada kai da masu ruwa da tsaki wajen ganin an shawo kan al’amuran, hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen daukar matakan da suka dace kan duk wani ma’aikacin gwamnati da ya yi kasa a gwiwa.

Sannan yace an shigar da kara, kwamitin ofishin ya bincika kuma aka same shi da laifin yin amfani da sa’o’in aiki na hukuma don kasuwanci masu zaman kansu.

“Mun zo nan ne domin wayar da kan ma’aikatan gwamnatin tarayya kan muhimmancin bayyana kadarorin da kuma tabbatar da cewa mun bi ka’ida.

“Mun kuma wayar musu da kai kan ka’idojin da’a na jami’an gwamnati domin su san ‘ayyukan su da abin da ba su yi ba tare da alhakin da ya rataya a wuyansu.

“Ba ma sa ran kowane mutum zai fahimce mu nan take amma muna da kwarin gwiwar cewa Shugabannin Ma’aikatu daban-daban za su taimaka wajen fayyace saƙonmu ga mutanen da ba su fahimta ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *