Zulum ya raba tallafin abinci da sauran kayan buƙata ga mutum 2,000 a unguwar Feezan ta garin Maiduguri.

Gwamnan jihar Borno a Arewa maso Gabashin kasar, Babagana Umara Zulum, ya raba tallafin abinci da sauran kayan buƙata ga mutum 2,000 a unguwar Feezan ta garin Maiduguri.

Rabon kayan da ya gudana a kwalejin Mohammed Goni, wata hanya ce ta rage wa jama’ar jihar raɗaɗin janye tallafin man fetir da gwamnatin tarayya ta yi.

A cikin watan Yuli gwamna Zulum ya ƙaddamar da shirin bayar da tallafin da nufin taimakawa iyalai dubu 300.

A karkashin shirin mazauna unguwar Feezan sun samu tallafin kayan abinci da sauran kayan buƙata, bayan tantance su domin tabbatar da cancantar su.

Kwamishinan harkokin ƙananan hukumomi da masarautun jihar Borno, Sugun Mai Mele, ya ce unguwanni 15 ne za su amfana da wannan tallafi a cikin Maiduguri, kuma kowacce unguwa za ta samu buhun shinkafa 2,000 da kuma buhun wake 2,000.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *