SERAP ta maka Akpabio da Tajudeen Abbas a kotu kan abinda ta kira haramtaccen shirin kashe Naira biliyan 40 domin sayen motocin silke 465

Hukumar dake fafutukar yaki da cin hanci da rashawa tare da Kare Hakkokin Tattalin Arziki SERAP ta maka shugabanin Majalisar Dokokin kasa Godswill Akpabio da Tajudeen Abbas a kotu kan abinda ta kira haramtaccen shirin kashe Naira biliyan 40 domin sayen motocin silke 465 da kuma Naira biliyan 70 a matsayin tallafi wa yan majalisar.

Karar ta zo ne a daidai lokacin da Shugaban Majalisar Dattawa Godswill Akpabio ya bayyana wa duniya cewa, akawun Majalisar Magaji Tambuwal ya aikawa wa ‘yan Majalisar da alawus na hutu yayin da ‘yan Najeriya ke fama da matsanancin talauci.

SERAP ta ce kididdiga ta nuna cewa mutane miliyan 137 ne ke fama da mumunan rashi da talauci, saboda haka ta ke so a dakatar da Majalisar daga kashe wadanan makudan kudade domin ya saba wa kundin tsarin mulkin kasa da kuma hakkokin bil’adama na duniya.

A nasa bayanin, gagarabadan Majalisar Dattawa, Ali Ndume, ya ce wannan abu da ake cece-kuce akai, abu ne da aka saba yi a Majalisa. Ya ce tunda aka fara dimokradiya a Najeriya ake saya wa ‘yan Majalisa motoci domin yin aiki, kuma haka ake biyan su albashin su da hakokkin su, saboda haka ba sabon abu ba ne.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *