Emefiele ya bayyana a gaban kotu domin amsa zargi kan tuhume-tuhume 20 da ake masa da suka shafi rashawa.

Gwamnan babban bankin kasa -CBN da aka dakatar, Godwin Emefiele ya bayyana a gaban kotu a yau Alhamis domin amsa zargi kan tuhume-tuhume 20 da ake masa da suka shafi rashawa.

Lauyoyin gwamnati ne suka shigar da sabobbin zarge-zarge a kansa da suke da nasaba da ‘amfani da ofishinsa wajen bayar da kwangila ba bisa ka’ida ba’,

Ana zargin Emefiele da hada baki da wata ma’aikaciyar babban bankin kasar da kuma wani kamfani wajen siyo motoci masu sulke 98 ba tare da sun bi ka’idojin bayar da kwangila ba.

Rahotanni sun ce matar da ake zarginsu tare darekta ce a bankin na CBN kuma kawo yanzu ba su mayar da martani ba kan wadannan zarge-zargen.

A watan Yuni ne Shugaba Bola Tinubu ya dakatar da Emefiele kuma hukumomi suka gabatar da shi gaban kuliya a Lagos bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba ko da yake ya musanta zargin.

Sai dai alƙalin kotun, mai shari’a Hamza Muazu ya ɗage zaman zuwa ranar 23 ga watan Agustan 2023 saboda rashin bayyanar Sa’adatu Yaro, wata jami’a da ake zargin sun aikata laifin tare da Emiefele.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *