Mutuwar sojojin da helikwaftansu ya faɗo a Neja babbar asara ce mai tayar da hankali ga Najeriya – Tinubu

Shugaba Bola Tinubu ya bayyana mutuwar wasu sojojin ƙasarnan da helikwaftansu ya faɗo a  jihar Neja, a matsayin ‘babbar asara mai tayar da hankali’ ga Najeriya.

A ranar Litinin ne wasu sojojin ƙasar suka mutu lokacin da jirgin da suke ciki ya faɗo a ƙauyen Chukuba kusa da ƙaramar hukumar Shiroro a jihar Neja

Tinubu yace sojojin na kan aikin hidimtawa ƙasar sune lokacin da suka gamu da ajalinsu.

Tunda farko rahotanni sunce jirgin na aikin kwashe sojojin da suka jikkata ne a fagen daga don kai su asibiti, lokacin daya faɗo ƙasa, tare da kashe waɗanda ke cikinsa.

Wannan dai, shine karon farko da gwamnatin tarayya ta fitar da sanarwa akan mutuwar sojojin ƙasar da kafofin yaɗa labarai suka yita bada rahotanni a jihar Neja.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *