Kungiyar Dattawan Arewa ta shawarci Tinubu daya gaggauta janye duk wani takunkumin da aka kakabawa Nijar

Kungiyar Dattawan Arewa ta shawarci shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu daya gaggauta janye duk wani takunkumin da aka kakabawa Jamhuriyar Nijar sannan a cigaba da tattaunawa.

Idan ba’a manta ba, Nijeriya ta rufe dukkannin iyakokinta da Jamhuriyar Nijar, sannan kuma ta katse wutar lantarki dadai sauran takunkumai.

A wata sanarwa da Daraktan Yada Labarai da hulda da Jama’a na kungiyar, Dakta Hakeem Baba Ahmed ya fitar a Abuja, ya shawarci Nijeriya data cire duk wani takunkumin da aka sanyawa Nijar, da nufin tilastawa gwamnatin Sojin kasar dasu mika wuya ga bukatar ECOWAS.

Dakta Hakeem ya kara da cewa, ya kamata shugaba Tinubu ya tabbatar da “tsaron lafiyar shugaba Bazoum da iyalansa da kuma maido da tsarin mulkin Dimokuradiyya su Kungiyar kuma tayi watsi da bukatar amfani da karfin soji wajen dawo da mulkin Dimokuradiyya a Jamhuriyar Nijar inda ta ce, yin hakan ba zai haifar da kyakkyawan sakamako ba

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *