Gwamna Makinde ya buƙaci baiwa ‘yan siyasa shekaru 6 A duk wa’adi

Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya bayar da shawarar a yi wa ‘yan siyasa wa’adi daya na shekaru biyar ko shida.

Makinde ya ce ya kamata ‘yan siyasa su yi koyi da shugabancin kungiyar Pentecostal Fellowship of Nigeria (PFN) na wa’adi daya.

Ya na mai da martani ne ga shugaban PFN na kasa, Bishop Wale Oke na cewa shugabancin hukumar ba ya bada damar sake tsayawa takara karo na biyu.

Oke ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi a wurin bude taron kungiyar PFN ta kasa a Ibadan.

Sai dai da yake jawabi a wurin taron, Makinde ya ce ya kamata ‘yan siyasa su yi koyi da PFN, yana mai jaddada cewa shekaru hudu ba za su isa a cimma burin mutum ba.

A cewar Makinde: “A karon farko na ji cewa babu wa’adi na biyu a PFN. Wataƙila, muna bukatar mu koyi abubuwa ɗaya ko biyu daga wannan tsarin ga al’ummarmu.

“Ni mai goyon bayan tsarin wa’adi guda ne. Hasali ma bana son wani wa’adi na biyu kuma na ce wa ubannin imani shekaru hudu ba su isa ku yi duk abin da kuke so ku yi ba ya isa ku yi tasirin ku kuma ku bi hanyar ku.

“Idan muka sami damar tattauna wannan, ina ganin shekaru biyar ko shida na wa’adin mulki, watakila shekaru biyar, za su wadatar da yawancinmu mu yi duk abin da ya kamata mu yi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *