CBN ya lashi takobin billo da  sabbin matakai don magance faɗuwar darajar naira

Babban Bankin kasa CBN ya lashi takobin billo da sabbin matakai don magance faɗuwar darajar naira a kasuwar sauyin kuɗi.

Matakan na zuwa ne bayan ganawar da Shugaba Bola Tinubu ya yi da Muƙaddashin Gwamnan CBN, Folashodun Shonubi a fadar shugaban kasa.

Da yake ganawa da yan jaridar fadar shugaban kasa Mista Shonubi ya bayyana damuwa kan halin da ƙudin ƙasar nan ke ciki a kasuwar canji ta duniya, lamarin da ya ce zai yi aiki don magancewa.

yace shugaba Tunubu ya damu sosai da abubuwan da ke faruwa a kasuwar canjin, sannan ya nuna damuwa mautuka akan rayuwar talaka a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *