Barazanar da NLC tayi na tafiya yajin ba tare da bada wata sanarwa ya janyo cece kuce tsakanin ‘yan Najeriya

Barazanar da kungiyar NLC tayi na tafiya yajin ba tare da bada wata sanarwa ba muddin yan kasuwa suka kara kudin man fetur ya janyo cece kuce tsakanin wasu daga cikin aulumar kasar nan.

Da yawa daga cikin yan Najeriya sun nuna shakku akan barazanar kungiyar ta NLC tare da cewa mai jiya ma tayi balle yau.

Ko a zanga zangar da kunghiyar ta NLC ta fara a makonnin da suka gabata da yawa daga cikin Yan Najeriya sukaki amsa kiran kungiyar saboda abinda suka kira zanga zangar ba zatayi tasiri ba.

Yan Kwadagon sunyi wannan barazana ne bayan da yan kasuwa da gwamnatin tarayya sukayi barazanar kara farashin man fetur a mako mai zuwa muddin farashin Dala bai sauko kasa daga naira 950 ba.

Yan kasuwar sunce karin farashin na man fetur zai tashi daga naira 617 zuwa 720 zuwa 750.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *