“Muna tunanin ɓullo da hanya na magance matsalar tsaro da ya dabai-baye arewa”. – Gwamnonin Arewa

Gwamnonin shiyyar arewa ta tsakiya sun ce suna tunanin ɓullo da wata hanya na magance matsalar tsaro da ya dabai-baye yankin arewa.

Gwamnan jihar Plateau, Caleb Mutfwang shi ya bayyana haka lokacin da ya karɓi bakuncin kwamitin majalisar wakilai da yake gudanar da bincike kan badakalar naira tiriliyan 2.3 na kuɗaɗen asusun tallafawa manyan makarantu na (TETFUND) a Jos a karshen mako.

Mutfwang ya faɗa wa kwamitin wanda ya samu jagorancin Unyime Idem cewa gwamnonin shiyyar za su yi magana da harshe ɗaya kan matsaloli da suke fuskanta, musamman rashin tsaro.

Duk da cewa gwamnan bai yi wani ƙarin haske ba kan irin shirin da suke yi, ya ce shi da takwarorinsa za su tashi tsaye don ganin an samar da ƴan sandan jihohi.

Ya yi kira ga majalisar wakilan Najeriya da su goyi bayan duk kudurori da aka kawo waɗanda suka danganci tsaro.

Jihohin arewa ta tsakiya sun kunshi Benue, da Plateau, da Nasarawa, da Niger da Kwara, inda shiyyar ta kasance ɗaya daga cikin wadda ke fama da matsalar tsaro a ƙasar nan.

Rikicin manoma da makiyaya na cikin abubuwan da suke yi wa shiyyar babbar barazana.

Ko a farkon watan nan, rahotanni sun bayyana cewa an kashe mutane 21 a wani hari da wasu suka kai kauyukan jihar Plateau.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *