Saraki ya bayyana kaduwarsa kan yadda likitocin Najeriya ke aiki na tsawon sa’o’i 100 a cikin mako 1

Tsohon shugaban majalisar dattawa, Dakta Bukola Saraki ya bayyana kaduwarsa kan yadda likitocin Najeriya ke aiki na tsawon sa’o’i 100 a cikin mako guda.

Ya bayyana hakan ne a lokacin da jami’an kungiyar likitoci ta kasa NARD suka kai masa ziyara, bayan dakatar da yajin aikin da suke yi.

An bayyana cewa Saraki ya yabawa likitocin kan matakin da suka dauka na janye yajin aikin.

A cewar tsohon shugaban majalisar dattawan, wanda kuma likita ne, “abin da ya fi ba shi mamaki shi ne yadda da yawa daga cikin ‘ya’yan kungiyar ke yin aiki sama da sa’o’i 100 a kowanne mako.

Ya yaba wa likitocin da suke aiki a cikin mawuyacin hali, tare da yaba musu game da yadda suke nuna kishin kasa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *