NUJ reshen jihar Zamfara ta bukaci gwamnatin tarayya da su kawo karshen sace-sacen mutane da akeyi a jihar.

NUJ reshen jihar Zamfara, ta bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar da su kawo karshen kashe-kashe da sace-sacen mutane da ba su ji ba ba su gani ba a jihar.

Kungiyar ‘yan jaridu ta Najeriya NUJ reshen jihar Zamfara, ta bukaci gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar da su kawo karshen kashe-kashe da sace-sacen mutane da ba su ji ba ba su gani ba a jihar.

Kungiyar ta lura cewa lamarin ya zama abin kunya ta yadda ‘yan kasa suka daina samun isasshen barci saboda rashin kwanciyar hankali.

Kungiyar ‘yan jaridun, a cikin sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta, Kwamared Ibrahim Musa Mazere da sakatare, Kwamared Ibrahim Ahmad Gada, ta koka da yadda ‘yan ta’addan ke gudanar da ayyukansu kamar babu gwamnati.

NUJ ta kuma bukaci Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin Jihohi da su rubanya kokarinsu wajen ganin an magance matsalar rashin tsaro da ke kunno kai a sassan kasar nan.

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnatin jihar da ta gaggauta samar da managartan tsare-tsare da za su iya rage radadin da talakawa ke ciki.

Sai dai kungiyar ta yabawa kudurin Gwamna Dauda Lawal na bullo da asusun bada tallafin tsaro na jihar a wani bangare na matakan da gwamnatinsa ke dauka na magance matsalar rashin tsaro a jihar, inda ta shawarci gwamnatin jihar da ta kafa kwamitin tsaro wanda ya hada da shugabannin gargajiya, da jami’an tsaro da suka yi ritaya da  sauran masu ruwa da tsaki.

Kungiyar ta NUJ ta kuma tunatar da Gwamnan, alkawarin da ya yi a baya na gina cibiyar yada labarai da ta dace da matsayin kasa da kasa a jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *