Majalisar wakilai ta hana daukar mutum 300 aiki da hukumar JAMB ke shirin yi

Kwamitin Majalisar Wakilai da ke binciken badakalar ayyukan yi a ma’aikatu, da hukumomin gwamnati ya dakatar da daukar ma’aikata 300 da hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB ke shirin yi.

Kwamitin ya hana daukar aikin  ne saboda yadda mahukuntan hukumar suka yi amfani da son kai wajen tallata mukaman.

An bayar da wannan tabbacin ne a ranar Litinin lokacin da magatakardan JAMB, Ishaq Oloyede, ya bayyana a gaban kwamitin.

Oloyede ya sanar da kwamitin cewa hukumar ta gudanar da atisayen daukar ma’aikata guda 5000 tsakanin shekarar 2015 zuwa 2023 domin cike guraben da aka samu saboda ritaya.

Mun yi amfani da cancanta ne saboda mun yi imanin cewa mafi kyawun lokacin da yanayin aikinmu ya cancanci hakan.

Idan za mu yi tallace-tallace wajen daukar mutum 300 aiki ba za mu iya samun da abin da muke bukata ba.

Na yi imani cewa ya zama dole a lokacin da muka dauki ma’aikata mu san kwarewarsu a aiki

Amma Idan muka yi talla zamu iya daukar wanda bai cancanta aiki ba ba tare da mun sani ba kuma ina tabbatar masu da cewar haka muka yi in ji Oloyede.

Shugaban kwamitin, Yusuf Gagdi, ya ce matakin da hukumar ta JAMB ta dauka na daukar ma’aikata ba tare da talla ba ya saba wa doka.

Me ya sa kuke tunanin tallan ba zai fi kyau ba? Kuna da ikon tantance mutanen da suka nema don samun ingantattun mutane don yin waɗannan ayyukan.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *