Kwastam ta cafke haramtattun kayayyaki na naira miliyan N17m

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta ce ta kama buhunan shinkafa da aka shigo da su daga kasar waje guda 203, motoci biyar, da harsashi 1,245 da kudinsu ya kai Naira miliyan 17 da aka yi watsi da su a hanyar daji dake karamar hukumar Yewa ta Arewa a jihar Ogun.

Kwanturolan yankin na jihar, Bamidele Makinde, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Abeokuta ranar Litinin.

Ya ce, “Da misalin karfe 00:24 na ranar Juma’a, 12 ga watan Agusta, 2023, Rundunar Roving B ta kama wasu tsofaffin motoci guda biyar, (Toyota Camry mai dauke da lamba 4TIBG22KIWU312145, sannan da wata Toyota Camry mai lamba 4TIXK1263NU108237.

Kazalika “Akwai Motocin Mazda 626 uku masu dauke da lamba JM2GD14H201568566, JMZGF14F201173029, da kuma JMZGF14P20141862 bi da bi), makare da lodi buhunan shinkafa 203 ta kasar waje mai nauyin kilogiram 50kg kowace an watsi dasu a mahadar hanyar Tobolo dake kusa da Jamhuriyar Benin da kuma kusa da Ijoun ta karamar hukumar Yewa ta Arewa a Jihar Ogun, Najeriya.”

Bamidele ya kara da cewa, a yayin da rundunar ke binciken motocin da aka kama, ta gano cewa an boye alburusai masu rai a cikin buhunan shinkafa 20.

A cikin kalamansa, “A yayin da ake gudanar da binciken motocin da aka kama, an gano harsasan na Lion, Trust, Supreme da Redstar kimanin 1,245 na 70mm (2¾), an boye su cikin basira a cikin buhuna 20 na wadanda aka kama na shinkafar kasar waje.”

Bamidele ya ce an ajiye kayayyakin ne domin adanawa yayin da aka fara bincike don gano masu fasa-kwaurin.

“Kudin da aka biya na harajin alburusai da shinkafa ya kai N17,638,145.00 an ajiye kayayyakin ne domin adanawa, har sai an dauki matakin da ya dace.

“Ana ci gaba da gudanar da bincike don bankado kungiyar da ke da alhakin yunkurin safarar kayayyakin don kamawa da gurfanar da su,” in ji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *