NEMA ta ƙaddamar da rarraba kayan tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a 2022

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta ƙaddamar da rarraba kayan tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a 2022 da kuma mabuƙata a jihar Kano da ke arewacin ƙasar.

Shugaban hukumar, Mustapha Ahmed-Habib, ya ce suna sa ran raba kayan ga iyalai 660,000 a faɗin Najeriya.

Mataimakin Gwamnan Kano Aminu Abdulsalam-Gwarzo, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf a rabon kayan ranar Asabar, ya ce iyalai 979 ne za su amfana daga ƙananan hukumomi 20 na Kano, yayin da aka ware wa ƙananan hukumomin Municipal da Tarauni 1,520 kowacce.

Cikin kayan abinci da aka raba akwai shinkafa, da wake, da dawa, da kayan miya, da gishiri, da kuma sinadaran ɗanɗano.

Kazalika, an raba kayayyakin noma da na inganta rayuwa kamar gidan sauro, da ledoji, da barguna, da katifu, da botikai na roba, da risho, da tukunyar girki. Aminu Abdulsalam ya nemi waɗanda suka amfana da tallafin da kada su sayar da su, yana mai cewa an ba su ne don su inganta rayuwarsu

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *