FRSC: Jimillar mutum 4,387 ne suka mutu sakamakon haɗurran ababen hawa cikin wata shidan farko na 2023 a Najeriya.

Jimillar mutum 4,387 ne suka mutu sakamakon haɗurran ababen hawa cikin wata shidan farko na 2023 a Najeriya, a cewar hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa.

Jami’in faɗakarwa na hukumar Federal Road Safety Corps (FRSC), Bisi Kazeem, ya faɗa wa kamfanin labarai na Najeriya NAN cewa daga watan Janairu zuwa Yunin 2023 an samu mutum 14,108 da suka ji raunuka.

A lissafi na tsakatsaki, alƙaluman na nufin mutum 731 ne ke mutuwa duk wata, ko kuma 24 a kowace rana, a cewar rahoton na NAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *