Tinubu ya taya matasan Nigeria murnar ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware musu.

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya matasan Nigeria murnar ranar da Majalisar Dinkin Duniya ta ware musu.

Cikin wani saƙo da ya wallafa shafinsa na Tuwita, shugaba Tinubu ya ce ”A yayin da matasqn Nigeria su ke bikin ranar Matasa ta Duniya, su sani cewa ilahirin ƙasarnan na tare da su, domin taimaka mu su cimma burukansu.

Tinubu ya kuma yi kira ga matasan da su yi ƙoƙari wajen fuskantar ƙalubalen da ke gabansu, domin cimma nasarori a rayuwarsu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *