“Kiran ‘yan ƙasar ke yi mana da muyi juyin mulki “tsananin rashin kishin ƙasa ne da kuma mugunta” – Sojin Najeriya

Rundunar Sojin Najeriya ta ce kiran da wasu ‘yan ƙasar ke yi mata da ta yi juyin mulki “tsananin rashin kishin ƙasa ne da kuma mugunta”.

Hedikwatar tsaron ta Najeriya ta ce tana mayar da martani ne sakamakon kiraye-kirayen da wasu ke yi suna fakewa da rashin kula da walwalar dakarunta.

A cikin wata sanarwa da Birgediya Tukur Gusau ya fitar ya ce Hedikwatar tsaro ba ta jin daɗin kiraye-kirayen da ake yaɗawa a intanet game da walwalar dakarunta ba.

A don haka ya ce sun yi tir da yunƙurin wasu na neman Rundunar Sojin Najeriya mai bin doka, ta sauya gwamnati a ƙasar nan ba ta hanyar da tsarin mulki ya tanada ba Birgediya Janar Tukur Gusau ya ce su na tabbatarwa ƙarara cewa rundunar ta gamsu kuma ta fi son zama a ƙarƙashin mulkin dimokuraɗiyya, kuma ba za ta yi wani abu da zai kawo wa dimokuraɗiyya cikas ba.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu, a matsayinsa na shugaban ƙungiyar raya tattalin arzikin Afirka ta Yamma (Ecowas), shi ne ke jagorantar yunƙurin tilasta wa sojoji su mayar da Shugaba Bazoum Mohamed kan mulki da ƙarfin tsiya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *