A yau ne Rahma Redio ta Kano ta cika shekaru 12 da fara gabatar da shirye shirye

A yau ne tashar Rahma Radio ta Kano ta cika shekaru goma sha biyu da fara gabatar da shirye shirye a matsayin kafar yada labarai mai zaman kanta.

Kafar ta Rahma wadda aka samar karkashin manufofin samar da ci gaban al’umma, da bunkasa harkokin rayuwar da suka kunshi ilimi, noma da tattalin arziki har ma da zaburar da al’umma muhimmancin sanin kai, ta fara gabatar da shirye shiryen ta ne a ranar 12 ga watan Agusta shekara ta 2011 a lissafin miladiyya wadda ta kasance ranar Juma’a.

A wancan lokaci ana gabatar a shirye shirye ne akan mita 97 da digo 7 a zangon FM wanda daga bisani aka koma mitar da ake kai yanzu ta 97 da digo 3 duk dai a zangon na FM.

Idan mai sauraro zai iya tunawa, a ranar da aka fara sauraran tashar ta Rahma a nan Kano, da yammacin ranar ta Juma’a, an sanya karatun AlQur’ani mai girma dake dauke da muryar Sheikh Ahmad Sulaiman UP SOUND AHMAD SULAIMAN (SURATUL FATIHA)

A tsawon wadannan shekaru goma sha biyu da tashar Rahma Radio tayi cikin gabatar da shirye shirye karkashin manufofin da suka sanya aka samar da ita, an samu nasarar cimma abubuwa masu tarin yawa, da suka shafi al’umma a fannonin rayuwa daban daban.

Haka zalika tashar ta Rahma Radio Kano, ta haifar da Karin kafofin yada labarai da suka hadar da tashar talabijin ta Rahma TV da kuma sabuwar tashar Rahma radio Abuja da a yanzu take da shekaru biyu da watanni biyar da fara gabatr da shirye shirye, wadda take kan mita dari da 4 da digo 1 a zangon FM.

Tuni dai al’umma suka fara aikewa da sakon taya murna da fatan alkhairi ga tashar Rahma Radio ta Kano bisa zagayowar wannan rana da kuma cikar shekaru goma sha biyu cikin gudanar a ayyukan ilimantarwa da fadakarwa da kuma nishadantar da al’umma.

Cikin sakon ta ga al’ummar dake sauraro da kallon tasoshin na Rahma, shugabar hukumar zartarwa ta rukunin kamfanonin rahma wadanda ke da mallakin Rahma Radio Kano da Abuja da kuma Rahma Tv, Hajiya Binta Abdullah Sarki Mukhtar ta bayyana godiyarta tayi ga Allah madaukakin Sarki bisa wannan dama da ya bayar na gudanar da ayyukan wadannan tasoshi.

Ta kuma yaba da irin gudunmawar da al’uma masu sauraro suke bayar wa, musamman malamai da masana a fannoni daban daban na rayuwa suke bayarwa ta fannin shirye shirye da kuma fashin baki kan al’amauran rayuwa, inda ta bukaci al’uma da su kara bada gudunmawar su wajen daukar nauyin shirye shirye da tallace tallace ta yadda ayyukan kafofin za su ci gaba da tabbata.

Hajiya Binta Sarki Muktar ta kuma yi kira ga al’uma da su kasance masu kiyaye ka’idojin rayuwa da kuma kula da bin doka ta yadda za’a samu ci gaban a fannonin rayuwa daban daban.

A karshe tayi addu’ar samun ci gaba da gudanar da ayyukan wadannan tasoshi cikin nasara da taimakon Allah SWT.

A ranar lahadi ne dai Shugabar kamfanin Rahma media group Hajiya Binta Sarki Mukhtar za ta tattauna da masu sauraro kai tsaye ta Rahma radio da rahma Talabijin da kuma rahma radio Abuja da misalin Karfe 8:30 na dare kamar yadda al’umma su ka Bukaci ganawa da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *