“Mun shirya tsaf don cika duk wani umarni da shugaban kasa zai bamu na kai hari Kasar Nijar”. – Rundunar sojojin saman Najeriya

Rundunar sojojin saman Najeriya ta ce ta shirya tsaf don cika duk wani umarni da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu zai ba su na kai hari Kasar Nijar.

Babban hafsan Hafsoshin rundunar mayakan saman Kasar, nan Air Marshall Hassan Bala Abubakar ne ya  bayyana hakan a wani babban taro da ya yi da dukan kwamandojin rundunar a yammacin jiya bayan kammala taron ECOWAS.

Air Marshal HB Abubakar ya ce rundunar za ta ci gaba da mika wuya da yin biyayya ga shugannin fararen hula a kowane lokaci, sannan za ta ci gaba da zama cikin shirin ko ta kwana.

Babban hafsan hafsoshin mayakan saman Najeriyar ya yi bayanin cewa yanzu haka abin da ke faruwa a Najeriya da ma makwabtanta a Afirka ta yamma wani sha’ani ne mai sarkakiya da ka iya tasiri kan yanayin siyasar yankin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *