IGP ga jami’an ‘yan sanda: “Idan kuka guji karbar cin hanci, mutane zasu kaunace ku”.

Sufeto Janar na yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun, ya yi kira ga jami’an rundunar yan sandan Najeriya da su guji karbar kudi da sauran ayyukan cin hanci.

Da rashawa domin kara daukaka martabar hukumar a yakin da ake yi na tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’umma.

An ruwaito IGP na cewa na kasance ina gaya wa jami’ai na cewa mutane suna son yan sanda amma idan kuka karbi rashawa daga hannun su sai su guje ku kuma su daina taimakon Ku.

Lokacin da kuke aikata rashawa kuna gaya wa Allah kada ka damu da ni zan iya karw kaina, kuma Allah ba zai damu da ku ba.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da jawabi a Kano ranar Juma’a bayan wani liyafa ta musamman da aka gudanar a rundunar yan sandan Kano inda ya kai ziyarar duba rundunar da sauran su.

IG ya kuma bayyana cewa daga yanzu za a yi karin girma a rundunar yan sandan bisa cancanta ne kawai tare da bayyana cewa ba za a kara samun karin girma na musamman ba.

Har ila yau ya bayyana cewa zai yi wa hukumar binciken manyan laifuka ta CID garambawul a matakin kasa inda ya nada wadanda suka cancanta kawai. Ya bayyana cewa za a kuma yi irin wannan a cikin dokokin jihar.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *