A yammacin jiya  Alhamis ne shugabannin kungiyar Ecowas ta gudanar da taron gaggawa a Abuja

A yammacin jiya  Alhamis ne shugabannin kungiyar Ecowas ta gudanar da taron gaggawa a Abuja babban birnin Najeriya domin dauykar mataki kan sojojin da suka gudanar da juyin mulki a Nijar.

Shugabannin ƙasashen Ecowas sun ba da umarni ga dakarun sojin ƙungiyar su ɗaura ɗamarar kai hari da yakar kasar ta Nijar, bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar.

Sanarwar da Omar Aliu Toure, shugaban hukumar Ecowas, ya karanta bayan taron sirri da suka gudanar, shugabannin ƙungiyar sun ba da umarnin bijiro da dakarun ko-ta-kwana na Ecowas da yiwuwar tilasta wa Nijar aiki da ƙudurorin ƙungiyar ƙasashen Saidai umarnin kar harin kasar ta Nijar ya janyo cece kuce da Allah Wadarai a tsakanin wasu yan Najeriya a shafukan sada zumunta na zamani tun daga daren jiya zuwa waye garin yau

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *