Sanusi II ya bayyana wa Tinubu abinda suka tattauna da sojojin da suka kwace mulki a Nijar.

Sarkin Kano na 14 kuma Khalifan Ɗarikar Tijjaniyya, Malam Muhammadu Sanusi II, ya bayyanawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu abinda suka tattauna da sojojin da suka kwace mulki a Jamhuriyar Nijar.

Khalifa Muhammadu Sanusi II ya yiwa Tinubu bayanin abinda suka tattauna da masu juyin mulkin Nijar ne gabanin taron ƙungiyar ECOWAS dake duba yiwuwar ɗaukar matakin soji a Nijar, shawarar data bar baya da kura.

Bayan dawowar Sanusi II daga Nijar ne ya ziyarci shugaba Tinubu a cikin dare inda yayi masa bayanin tattaunawarsa da jagoran gwamnatin sojin Nijar, Janar Abdulrahmane Tchiani.

Ganawar Sanusi II da shugaba Tinubu ta kasance ne bayan shugaban ƙasar ya gama tattaunawa da manyan malaman Musuluncin Najeriya kan taƙaddamar ta Nijar.

Khalifa Sanusi yakai ziyarar ce a ƙashin kansa, domin gujewa illar da rikicin na Nijar da matakin soji da kungiyar ECOWAS ke shirin dauka akan masu juyin mulki zai yiwa Nijar da babbar maƙwabciyarta Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *