Ranar 30 ga watan Agustan 2023 za a yanke hukunci kan karar da Matawalle ya shigar na a dakatar da bincike da ake masa

Alkalin babbar kotun tarayya da ke  zamanta a Abuja, Ahmed Mohammed ya sanya ranar 30 ga watan Agustan 2023 domin yanke hukunci kan karar da tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya shigar a gabanta bisa bukatar da a dakatar da bincikensa.

A cikin takarardar karar tana tuhumar hukumar tsaro ta  DSS, rundunar ‘yansanda, da hukumomin ICPC da EFCC, hukumar shige da fice ta kasa  da kuma Atoni Janar na kasa a matsayin masu karar Gwamna Matawalle.

Matawalle, wanda ya kasance daya daga cikin wadanda shugaban kasa Bola Tinubu ya mikawa Majalisar Dattawa sunansa don a nada shi a mukamin minista, ya nemi kotun data dakatar da masu kararsa ne bisa duba ga hukuncin da mai shari’a Alkali Aminu Aliyu ya yanke a ranar 31 ga watan Mayun 2023 Hukunci ya dakatar da duk wata hukuma kan bincike kai tsaye ga tsohon gwamnan ko iyalinsa ko mataimakansa a gudanar da gwamnatinsa dangane da yadda aka kashe kudaden gwamnatin

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *