Likitoci masu neman kwarewa sun bayyana sharuɗan dakatar da yajin aikinsu

Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa ta Kasa ta fitar da sanarwar fitar tsarin sauya ma’aikatan asibiti, da kuma biyan kudin horon lafiya na shekarar 2023 a matsayin mafi karancin sharudda na janye yajin aikin da ta fara a ranar 26 ga watan Yuli.

Shugaban NARD na kasa, Dokta Emeka Orji ne ya bayyana hakan a wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu a ranar Laraba.

Orji ya ce duk da cewa an dakatar da zanga-zangar da aka shirya yi a fadin kasar, kungiyar ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin sa’o’i 72 domin ta biya wasu bukatunta na gaggawa na janye yajin aikin da take yi.

A cewarsa, kungiyar za ta yanke shawarar ci gaba ko janye yajin aikin daga ranar Juma’a 12 ga watan Agusta.

Likitocin da ke yajin aikin tun da farko sun shirya fara zanga-zangar lumana a kowace rana, daga ranar Laraba 9 ga watan Agustan 2023, idan gwamnati ta kasa biya musu bukatunsu.

Orji ya ce, “Mun yi taro mai muhimmanci a fadar Villa tare da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, don haka ba zai yi kyau a dauki irin wannan matakin ba, kuma washegari mu hau kan tituna don yin zanga-zanga, za a yi zanga-zanga. Kaga kamar akwai wata muguwar manufa a bayan bukatunmu.

Buƙatunmu na al’umma ne saboda akwai ƙarancin likitoci a asibitocinmu, don haka kaɗan daga cikin mu da suka rage muna yin aiki fiye da kima. Har yaushe za mu ci gaba a haka? Sun gaya mana abin da za su yi yau (Laraba), da kuma gobe (Alhamis), kuma muna fatan za su yi abu mai kyau.

Idan har za su iya yin wadannan abubuwa, to ina da tabbacin kwamitin zartarwa na kasa zai ba mu ikon dakatar da yajin aikin saboda mun fahimci juna.

Ka’idar maye gurbin kowane mutum guda ita ce ta farko kuma asusun MRTF na 2023 shine na biyu. Idan za su iya magance su, za mu yi kira ga mambobinmu da su dakatar da yajin aikin yayin da muke ci gaba da tattaunawa kan duk wasu basussukan albashin da ake bin su da sauran su.”

Orji ya ce bai kamata gwamnati ta yi wahala ba wajen aiwatar da maye gurbin kowane mutum tare da karin kudin ba.

Gwamnati tana da jerin sunayen wadanda suka fice kuma abu ne da za a maye gurbinsu nan take sannan kuma wadanda aka dauka ana biyansu albashin da kuka sanya kasafin kudin domin maye gurbin wadanda suka tafi.

“Don haka, ba shi da wahala aiwatarwa. Wannan abu ne da aka amince a yi tun watan Fabrairu amma ba a yi komai a kai ba, amma muna fatan gwamnati za ta yi kamar yadda aka amince da shi,” inji shi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *