Barau Jibrin ya tabbatar wa ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa jihohin Tiga da Gari daga jihar Kano cewa majalisar za ta yiwa kowa adalci a lokacin sake duba kudin tsarin mulkin shekarar 1999

Gabanin wani shirin sake duba kundin tsarin mulki, mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya tabbatarwa ‘yan kungiyar masu fafutukar kafa jihohin Tiga da Gari daga jihar Kano cewa majalisar za ta yiwa kowa adalci a lokacin sake duba kudin tsarin mulkin shekarar 1999

Sanata Barau ya bayyana haka ne a lokacin da ‘yan kungiyar karkashin jagorancin Sanata Mas’ud El-Jibrin Doguwa suka kai masa ziyarar ban girma a zauren majalisar a ranar Laraba.

Mataimakin shugaban majalisar, wanda ke shugabantar kwamitin majalisar dattijai kan sake duba kundin tsarin mulkin kasar, yace majalisar ta 10 zata baiwa  dukkanin kungiyoyin dake bada shawara a samar da jihohi da dama su gabatar da kararrakinsu.

Sanata Barau, a cewar wata sanarwa  ta hannun mai bashi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Alhaji Mudashir Ismail, ya yabawa ‘ya’yan kungiyar na jihohin Tiga da Gari bisa yadda suka cigaba da gudanar da ayyukansu tsawon shekaru.

Tunda farko, Sanata Doguwa ya jaddada bukatar samar da jihohi biyu daga jihar Kano, inda yace a cikin shekaru 40 da suka gabata, suna bada shawarar raba jihar Kano bisa la’akari da girmanta da yawanta domin a gaggauta ci gabanta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *