“Bamu yarda a afkawa Nijar da yaƙin ƙwatar dimokraɗiyya daga hannun sojojin mulki ba” -NSCIA

Majalisar Ƙoli ta harkokin Addinin Musulunci a Najeriya ta bayyana cewar bata goyon bayan ƙaƙabawa Jamhuriyar Nijar takunkumin karya mata tattalin arziki, kuma bata yarda a afkawa Nijar da yaƙin ƙwatar dimokraɗiyya daga hannun sojojin mulki ba.

Majalisar ta bayyana hakan a cikin wata  sanarwa data fitar, wadda Mataimakin Babban Sakataren majalisar, Salisu Shehu ya sanyawa hannu.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar ne shugaban majalisar, wadda tace bata goyon bayan ayi amfani da ƙarfin soja domin a kawar da sojojin juyin mulkin da suka hamɓarar da Gwamnatin Mohammed Bazoum, a cikin watan Yuli.

ECOWAS a ƙarƙashin shugaban ta, kuma Shugaban kasa Bola Tinubu, ta ƙaƙabawa Nijar takunkumin daya haɗa da rufe kan iyakokin Nijar da kuma kulle asusun duk wani ɗan uwa ko mai goyon bayan shugabannin mulkin sojan Nijar a dukkan Manyan Bankunan Kasashen ECOWAS.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *