Babbar mai sharia ta Jihar Kano Justice Dije Aboki ta bada umarnin a kawo karshen duk wata sharia data wuce shekara 2 ba a yanke hukuncinta kafin watanni 6 masu zuwa.

Babbar mai sharia ta Jihar Kano Justice Dije Aboki ta bada umarnin a  kawo karshen  duk wata sharia data wuce shekara  2 ba,a yanke hukuncinta  kafin watanni shida masu zuwa.

Justice Dije Aboki ta bada wannan umarni ne a lokacin da take jawabi a wajen taron karawa juna sani kan shugabanci da laifukan da suka shafi cin zali wanda kungiyoyin rajin kare hakkin bil adama suka shairya a Kano.

Tace tuni ta aika takardun zuwa ga kotunan Majerry a kano cewa dole ne duk shariun da sukayi jinkiri har zuwa shjekara biyu ba tare da yanke hukunci ko bada beli  to a gaggauta  kawo karshen irin wadannan shariu kafin wata shida .

Mai magana da yawun Kotunan Jihar Kano Baba Jibo Ibrahim yayi karin bayani.

Tun ranar rantsar da Justice Dije Aboki a ranar Litinin data gabata ta lashi takobin cewa da yardar Allah zata kawo sauyi a bangaren shari,a a jihar kano

Daya daga cikin kalubalen da ake fama dashi a bangaren na shari,a a kano harda jinkirin yanke hukunci da jan kafa da cin hanci da rashawa da sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *