Majalisar Dattawa ta tantance Festus Keyamo a matsayin minista

Majalisar Dattawa ta tantance Festus Keyamo daga jihar Delta a matsayin minista bayan dambarwar da ta mamaye tantacewar da farko.

Festus Keyamo ya bayar da hakuri a kan kuskurensa na baya, inda ya ƙi amsa gayyatar majalisa ta 9 kan ayyukansa a matsayin ƙaramin ministan ƙwadago.

A lokacin zaman tantancewar, Sanata Darlington Nwokocha daga jihar Abiya ya fargar da majalisar a kan yadda a baya Keyamo ya nuna “rashin ɗa’a” ga majalisa ta 9, inda ya zargi majalisar da aikata rashawa.

Tsohon ministan ƙwadagon ya bayar da hakuri sannan ya yi ƙarin haske kan abubuwan da suka faru a wancan lokacin.

Da farko dai Sanata Darlington ya nemi a dakatar da tantance Keyamo, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce har ya kai ga tsaiko ga aikin tantancewar.

Daga baya dai majalisar ta dawo ta kuma yafe masa laifin da ya yi a baya.

Festus Keyamo ne mutum na ƙarshe da majalisar ta tantance daga cikin 48 da Shugaba Bola Tinubu ya aike mata don amincewa da su a matsayin ministoci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *