Tinubu ya gana da gwamnonin da ke raba iyaka da Nijar

A ranar Lahadi ne shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnonin jihohin da ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Taron wanda ya gudana a fadar shugaban kasa da ke Abuja, wani bangare ne na tuntubar shugaban kasar kan halin da ake ciki a Nijar.

Daga cikin gwamnonin da suka halarci taron akwai Ahmed Aliyu (Sokoto), Umar Namadi (Jigawa), Mai Malam Buni (Yobe), Idris Nasir (Kebbi) da Dr Dikko Radda (Katsina).

Idan za a iya tunawa dai, shugaba Tinubu a matsayinsa na shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS, ya ba wa gwamnatin mulkin soja a jamhuriyar Nijar wa’adin kwanaki bakwai na su mayar da mulki hannun Mohammed Bazoum.

Bayan wa’adin, Tinubu a wani taro da ya gudanar a Abuja a karshen makon da ya gabata, ya kuma bayyana wasu takunkumin da ya sanya aka toshe iyakokin da suka hada Nijar, yayin da aka dakatar da tura wutar lantarki da jiragen sama.

Tinubu ya rubutawa shugabannin majalisar dokokin kasar amincewa da tura jami’an soji zuwa kasar Nijar mai fama da rikici amma ya samu shawarar a bi a hankali a halin da ake ciki yanzu.

Kungiyar zamantakewa da al’adu ta Ohanaeze Ndigbo, ta bukaci shugaban kasa Bola Tinubu ya dakatar da duk wani amfani da soji a Jamhuriyar Nijar.

Ohanaeze ta yi gargadin cewa ayyukan soji a jamhuriyar Nijar zai yi mummunar illa ga Najeriya saboda makwabciyar kasar na samun goyon bayan Rasha.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *