SERAP ta kai karar Tinubu zuwa kotu

Kungiyar tabbatar da daidaito da yaki da cin hanci da rashawa ta kasa SERAP ta kai karar shugaban kasa Bola Tunubu zuwa kotu abisa zarginsa da yin jin kiri wajen bayyana yadda ya kashe kudaden rara na tallafin man fetur naira miliyan dubu dari 4

Bayan makonni hudu da cire tallafin man fetur ne gwamnatin tarayya tace ta ajiye rarar kudi naira miliyan dubu dari 4 da a baya suke zurarewa a aljihun wasu yan tsirari da sunan tallafin fetur acewar Bola Tunubu.

Saidai bayan sanarwar samun rarar kudin ne yan Najeriya suka zuba idanu dan ganin yadda za,ayi da kudaden,yayinda gwamnatin ta Tunubu tace zata rabawa yan kasa kudin dan rage musu radadi tun a farkon watan da ya gabata.

Amma a karar ta SERAP takai babar kotun tarayya dake Lagos.tace ya zama wajibi kotun ta turasa shugaba Bola Tunubu ya wallafa hanyoyin da yabi wajen kashe wadancan matsutsan kudade naira miliyan dubu dari 4 na rarar man fetur.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *